Kasuwanci

Yadda faduwar darajar Naira ke yin illa ga kasuwanci a Najeriya

Informações:

Sinopsis

Shirin 'Kasuwa a kai miki dole' na wanna makon ya mayar da hankali akan faduwar darajar naira da ke ci gaba da yin illa ga harkokin kasuwanci a sassan Najeriya. Wakilinmu a jihar Kano Abubakar Abdulkadir Dangambo ya duba yadda matsalar ke yin tasiri musamman babbar kasuwar hatsi ta Dawanau da ke Kano, wadda ke tattara 'yan kasuwa daga Najeriya da kuma kasashe irin su Chadi da Kamaru da Nijar da Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.