Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Najeriya: Tsadar rayuwa ta tilastawa mutane satar abinci a rumbunan gwamnati

Informações:

Sinopsis

A Nageriya daidai lokacin da ake fama da fatara da kuma tsadar rayuwa,  jama’a sun bullu da wani sabon salo na yin wasoson abincin da aka jibge a cikin rumbunan da aka bayyana cewa mafi yawan su mallakar gwamnati ne  Abin tambayar shine, mecece makomar wannan bakuwar dabi’a da wasu ‘yan Najeriya suka bullo da ita a cikin wannan yanayi na fatara da kuma tsadar rayuwa?Wadanne matakai suka kamata a dauka domin shawo kan wannan matsala da ka iya rikidewa domin kasancewa barazana, hattama ga bangaren tsaron kasar.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.