Al'adun Gargajiya

Informações:

Sinopsis

Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

Episodios

  • Koken Jama'a a kan yadda hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi rikon sakainar kashi

    21/05/2024 Duración: 10min

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda Jama'a ke koken game da rikon sakainar kashi da hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi, kamar Makon jiya yau ma shirin ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya tattauna da shugaban kwamitin raya Al'adun Gargajiya na Majalisar dokokin Jihar, Hon. Sarki Aliyu Daneji.Ku latsa alamar sauti don jin yadda shirin ya kasance....

  • Yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Kano da ke Najeriya

    14/05/2024 Duración: 10min

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya yi duba a kan yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Karofin Kofar Mata wadda ke da dogon Tarihi.Shirin ya samu zarafin tattauna wa da Baballiya Hamisu, wanda shi ne mai magana da yawun Marinar ta Kofar Mata.

  • Yadda tsadar rayuwa ke barzana ga Maroka da Sankira a Jamhuriyar Nijar

    26/03/2024 Duración: 10min

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya duba yadda jama'a a Maradi suka koma amfani da ruwan randa a maimakon kankara lokacin azumin watan Ramadana, saboda tsadar kankarar. Akwai mu dauke da yadda Maroka da kuma Sankira ke fuskantar barazana a sakamakon tsadar rayuwa.Dannan alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.

  • Yadda masarautar Hausawan Turai ke gudanar da ayyukanta

    19/03/2024 Duración: 10min

    Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Sarkin Hausan Turai Alhaji Surajo Jankado Labbo da ke kasar Faransa, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi kan wasu batutuwa da suka shafi Hausawa.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........

  • Tasirin masu sarautar gargajiya wajen inganta tsaro a yankunansu

    05/03/2024 Duración: 10min

    A sakamakon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nigeria na 1976,  aka tsame hannun sarakunan gargajiya a kasar cikin sha’anin kula da harkokin tsaro da harkokin shari’ah  da kuma batun tara haraji a cikin al’ummarsu.Hakan ne ya sanya Sarakuna duk da kasancewarsu iyayen kasa, suka koma gefe inda suka zamo ‘yan kallo kan wadannan al’amura.  Amma yayinda gwamnatin Nigeria ke tunanin sake damka wa Sarakuna wannan dama, wasu daga cikin su fara bijiro da sabbin matakai da nufin tsare rayuka da dukiyar al’ummarsu daga ‘yan ta’adda.A baya bayan nan, Mai Martaba Sarkin Ningi a jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad ‘Danyaya, ya samar da wata katafariyar kungiyar tsaro ta ‘yan sa-kai, wacce ke karade sako da lungun yankin don yaki da miyagun iri.

  • Yadda kananan kabilu suka samu wakilci a masarautar Katsinar Maradi

    27/02/2024 Duración: 09min

    Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Katsina Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, inda Sultan Ahmed Ali Zaki ya fitar da wani tsari na nada kananan kabilu a mukaman wakilan al’ummarsu, don kara dankon zumunci tsakanin kabilu sannan da raya al’adun gargajiya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.Baya ga Fulani da Bugaje da ke zama 'yan gida, Sultan ya nada wakilan Adarawa, Zabarmawa da Tubawa.  Masarautar Katsinar Maradi dai yanzu ta zama madubi kuma abin koyi  a bangaren hadin kan al'ummar Nijar.

  • Shiri na musamman kan marigayi Salissou Hamissou

    20/02/2024 Duración: 10min

    Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon na musamman ne, wanda ya yi duba akan irin gudunmuwar da marigayi Salissou Hamissou ya bayar a bangaren al'adu, musamman a lokacin da ya ke gabatar da wannan shiri na Al'adunmu na gado.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.....

  • Yadda al'adar auren Zaga ke shudewa tsakanin kabilar Sayawa a Najeriya

    13/02/2024 Duración: 09min

    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda auren Zaga tsakanin al'ummar Sayawa ke komawa tarihi, salon al'adar da ke bayar da damar gadon mace ko kuma bayar da kyautar ta da sunan aure. Duk da tarin kabilun da ake da su a cikin jihohin Najeriya, kowace kabila na da irin nau’o’in al’adunta na gargajiya a fannonin rayuwa dabam dabam.Al’adun kan bambanta ne ta fuskar tsarin zamantakewa, ko ta fuskar auratayya da makamantarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....

  • Yadda wasu abincin gargajiya na bahaushe ke barazanar bacewa

    12/12/2023 Duración: 10min

    Shirin al'adunmu na gado na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda abinci gargajiya irin na Bahaushe ke bata sannu a hankali Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa

  • Yadda sana'ar rini ke bacewa sannu a hankali a arewacin Najeriya

    14/11/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Al'adun Gargajiya' na wannan makon tare da Abdullahi Issa ya maida hankali ne kan bacewar sanar gargajiya ta rini a jihar Kano dake arewacin Najeriya, kafin daga bisa shirin ya leka Maradi dake jamhuriyar Nijar.

  • Bikin cika shekara daya da sarkin Katsinar Maradi yayi da hawa kan karagar mulki

    07/11/2023 Duración: 10min

    Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya maida hankali ne kan cika shekara daya da sabon sarkin Katsinar Maradi,Mai Martaba Ahmad Ali Zaki Maremawa yayi kan karagar mulki. A dai ranar Asabar 5 ga watan Nuwambar shekarar da ta gaba ne aka nada Mai Martaba  Ali Zaki a matsayin Sultan na 2 na Katsinar Maradi. Shirin ya tabo batun nasarorin da sarkin ya samu a wannan lokaci da yayi yana jagoranci.Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa....

  • Bafaranshiya ta lashe kyautar iya gasa biredi ta duniya

    31/10/2023 Duración: 10min

    Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya tabo batun kyautar da matashiya 'yan Farsans ta lashe, inda ta zamo ta daya a duniya a wannan shekarar wajen iya gasa biridi. Tarihi dai ya nuna wannan ne karo na faro da mace ta taba lashe wannan kyauta. Haka nan, shirin ya kuma tattauna da masu ruwa da tsaki a bangaren kan wannan al'amari.Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........ 

  • Yadda za'a bunkasa harshen Kanuri da al'adun sa

    24/10/2023 Duración: 10min

    Shirin al'adunmu na gado na wannan mako ya duba wani babban taron kasa da kasa da aka gudanar kan habbaka harshen Kanuri da al'adunsa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa

  • Shekaru 30 na Sarkin Masarautar Zazzau Suleja

    17/10/2023 Duración: 10min

    Shirin Al'adunmu na wannan mako ya yada zango ne Masarautar Zazzau Suleja ta jihar Neja dake Najeriya domin shaida bikin murnar cika shekaru 30 na Sarkin Masarautar mai dimbin tarihi, Mallam Muhammadu Auwal Ibrahim, wanda ya kasance gwamnan jihar na farko na farar hula a jamhuriya ta biyu daga shekarar alif 979 zuwa alif 983.

  • Yadda sauyin zamani ke shirin batar da sana'ar wanzanci

    10/10/2023 Duración: 10min

    Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya yi duba ne kan sana’ar wanzanci, wacce ke cikin sana'oin gargajiya na Hausawa da ke cike da abubuwa na al’ajabi. Mafi yawancin wanzamai gadon sana’ar suke yi daga iyayensu, amma wani lokacin, ana samun wasu daga waje da suke sha’awar koyon sana’ar don su samu hanyar cin abici. Duk kuwa da yadda bincike ya nuna cewa sana’ar ba abar da mutum zai koya cikin sauki da sauri ba ce.  Sakamakon yanda ake samun sauyin zamani, yanzu wanzamai sun fara fuskantar kalubale na rashin tabbas a sana'arsu saboda fara bacewar sana’arsu. Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........ 

  • Yadda harshen Hausa ke samun karbuwa a jami'o'in Burkina Faso

    26/09/2023 Duración: 10min

    Shirin ala'dun mu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan taron inganta harshen Hausa da aka shirya a jami'ar Ouagadougou da ke Burkian Faso  Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa

  • Bukukuwan al'adun kabilar Dukkawa

    12/09/2023 Duración: 10min

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda kabilar Dukkawa na jihar Neja da ke tarayyar Najeriya suke gudanar da bukukuwan gargajiya na shekara-shekara. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa

  • An kaddamar da shirin farfado da salon kidan Duma a Nijar

    31/08/2023 Duración: 10min

    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin kidan Duma, guda cikin al'adun jihar Maradi da ke kokarin gushewa.  A wani kokari na dakile gushewar al'adu, gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta kaddamar da wani gangamin horar da matasa kidan Duma, salon kidan da ke da shahara a tsakanin garuruwan Hausawa.Akwai dai salo kala kala na kidin Duma da yanzu ke zama inda mata sun fi son gargajiya yayin bukukuwansu abin da ake kira Partyn kauyawa Tasi’u Bakwai ya mana filla filla ma’anar kidi irinsu adamulmula, yar sahabi da sauransu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............

  • An gudanar da bikin doya na shekara-shekara a Jamhuriyar Benin

    22/08/2023 Duración: 09min

    Shirin 'Al'adunmu na Gado' na wannan makon zai duba yadda aka gudanar ad bikin doya na shekara-shekara a Jamhuriyar Benin.  Ana gudanar da wannan biki na doya a duk shekara musaman a ranar 15 ga watan Agusta a garin Savalou dake Jamhuriyar Benin. Tun asali dai daya daga cikin kabilun yankin da aka sani da kabilar Salman ne ke shirya wannan bikin na gargajiya domin nuna godiya da samun damuna mai albarka.

  • Dangantakar arewacin Najeriya da wasu kabilun kudancin kasar

    15/08/2023 Duración: 09min

    Shirin Al'adunmu Na Gado na wannan maako ya kawo batutuwa  da dama da suka hada da irin dangantakar da ke tsakanin kabilun arewacin Najeriya da  na kudancin kasar. Mazauna arewacin Najeriya da akasarinsu yan kasuwa ne,na gudanar da harakokinsu na kai da kawo daga wani yankin zuwa wanin yankin daban,to sai dai wasusu a maimakon fatauci,ba sun rungumi almajiranci da iya sani da suke da shi da nufin korewa bakin kuda ta hanyar  zuwa kudancin kasar a wancan lokaci. 

página 1 de 2